Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Shabab Ta Yi Ikirarin Kai Hari a Somaliya


Adadin wadanda su ka mutu sanadiyyar harin da aka kai jiya Lahadi, da kuma samamen da ya biyo baya na tsawon sa’o’i, a wani otal da ke gabar ruwa a kasar Somaliya, ya haura zuwa 15. Kungiyar al-Shabab ta yi ikirarin kai harin.

Jami’ai da kuma shaidu sun gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, gab da karfe 6pm agogon yankin, wata mota shake da bama bamai ta tarwatse a harabar otal din Elite da ke shahararriyar gabar nan ta Lido. Ba da dadewa ba, sai wasu ‘yan bindiga hudu suka afka cikin otel din.

Nan da nan sai jami’an tsaro su ka iso, su ka maye gurbin masu gadin otal din, wajen fafatawa da manharan.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Yada Labaran kasar, Ismail Muktar, ya ce duka maharani hudu da su ka afka cikin otal din sun halaka.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG