KADUNA, NIGERIA - Wannan ne dai karno farko da gwamnatin jihar Kaduna ta nada Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Amirul Hajj tun bayan nada shi Sarkin Zazzau, ya kuma bayyana cewa, abubuwan da ya gani na gazawa a aikin Hajjin na bana su na da sosa rai.
Mai Martaban wanda ke jawabi ga al'ummar masarautar Zazzau bayan dawowarsa daga kasa mai-tsarki ya ce shi kanshi sai da ya raba tawagar shi gida uku.
Dama dai tun kafin tashi zuwa kasar Saudiya a bana, an sami takun saka tsakanin Shugaban Hukumar Alhazan jihar Kaduna, Malam Yusuf Yakub Arrigasiyyu da Hukumar Alhazai ta kasa akan matsalar wasu kujerun masu kudin adashe, sakamakon jinkirin da aka samu wajen samun takardar izinin zuwa Saudiyya wato 'Visa'.
Jinkirin jigilar Alhazan jihar Kaduna don dawowa Najeriya dai na cikin matsalolin da Mahajjata da dama su ka nuna damuwa tun suna Saudiya.
Duk da nasarar da aka samu wajen jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki a bana dai, an ci karo da matsalolin masaukai a Makka da Madina da kuma Mina, sannan kuma dawo da Alhazan zuwa Najeriya shima na shan korafe-korafe saboda rashin sauri.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna