Gidan talabijin na ABC News ya amince da bayar da kudi dala miliyan 15 ga dakin karatu na zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump na fadar shugaban kasa, domin sasanta wata shari'a kan kalaman da George Stephanopoulos ya yi a talabijin, da suka shafi karar da mawallafiya E. Jean Carroll ta shigar kan Trump, kamar yadda wata takardar bayani ta kotu ta bayyana a jiya Asabar.
Karar wadda aka shigar a ranar 19 ga watan Maris a Kotun Gunduma ta Amurka da ke Kudancin Florida, ta zargi Stephanopoulos da yin wadannan kalamai da mummunar manufa da kaucewa gaskiya.
Sanarwar ta ce an yada kalaman ga wasu bangarori na daban, kuma an yi ta sake maimaita su.
Mai Magana da yawun gidan talabijin din na ABC News ya fada a wata sanarwa cewa, "Mun yi farin ciki da cewa bangarorin sun cimma yarjejeniya don yin watsi da karar kan sharuddan da aka gindaya a kotu."
Karar ta Ambato wata hira da aka yi da ‘yar majalisar wakilan Amurka Nancy Mace a ranar 10 ga watan Maris, ‘yar jam’iyyar Republican wacce ta yi magana a bainar jama'a game da fyade da aka yi mata tana matashiya.
A yayin tattaunawar, Stephanopoulos ya ce an sami Trump da laifin fyade kuma ya tambaye ta yadda za ta amince da goyon bayan dan takarar.
Daga cikin tanade-tanaden sasantawar, ya zuwa yau Lahadi, tilas ABC News za ta wallafa wata sanarwa a kasan bayanan da aka wallafa a ranar 10 ga watan Maris da suka biyo bayan tattaunawar.
Dandalin Mu Tattauna