Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baiwa Shugaban Argentina Shaidar Zama Dan Kasar Italiya Ya Janyo Cece-Kuce


Argentina's President Javier Milei visits Rome
Argentina's President Javier Milei visits Rome

Labarin da aka watsa a kafafen yada labaran Italiya, ya haifar da kakkausan martani daga wasu 'yan siyasa da kuma a kafofin sada zumunta na internet.

Gwamnatin kasar Italiya ta bai wa shugaban kasar Argentina Javier Milei shaidar zama dan kasa saboda tushen danginsa na Italiya, kamar yadda wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta fada a jiya Juma'a, tana mai tabbatar da rahotannin da kafafen yada labarai suka bayar.

Milei ya tafi birnin Rome ne domin ganawa da Firai Ministan Italiya Giorgia Meloni, da kuma halartar bikin shekara-shekara na ‘yan uwansa na Italiya a ranar Asabar.

Majiyar ta ce gwamnati ta bai wa shugaban na Argentina takardar zama dan kasar Italiya, amma kuma ba ta ba da cikakken bayani ba.

Labarin da aka watsa a kafafen yada labaran Italiya, ya haifar da kakkausan martani daga wasu 'yan siyasa da kuma a kafofin sada zumunta na internet, inda mutane ke kalubalantar bai wa Milei shaidar zama dan kasa, a daidai lokacin da aka kasa biyan bukatun 'ya'yan bakin haure da aka haifa a Italiya.

Dokokin zama dan kasa na Italiya sun dogara ne kan dangantakar jini, ma'ana ko da zuriyar ɗan Italiya da ke da nisa, na iya samun fasfo na kasar ta Italiya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG