Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Ta Shiga Yarjejeniyar Kasuwancin Yanki Pacific Ta CPTPP


A bara Birtaniya ta bayyana cewa za ta shiga cikin wannan babbar yarjejeniyar ciniki tun bayan ficewar ta daga Tarayyar Turai.

A hukumance, yau Lahadi kasar Biritaniya ta zama mamba ta 12 ta yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashen yankin tekun Pasifik, da ta hada da kasashen Japan, Australia da Canada, yayin da take kokarin kara zurfafa huldar da ke tsakaninta da yankin, tare da kulla huldar kasuwancinta a duniya bayan ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.

Birtaniya ta bayyana a bara cewa za ta shiga cikin wannan babbar yarjejeniyar ciniki tun bayan ficewar ta daga Tarayyar Turai.

Shigar ta Biritaniya na nufin cewa daga yau Lahadi, za ta iya amfani da dokokin kasuwanci na yarjejeniyar, da rage haraji tare da kasashe takwas daga cikin mambobin kasashe 11, wato Brunei, Chile, Japan, Malaysia, New Zealand, Peru, Singapore, da Vietnam.

Yarjejeniyar za ta fara aiki da kasar Australia a ranar 24 ga watan Disamba, kuma za ta yi aiki tare da mambobi biyu na karshe, wato Canada da Mexico, kwanaki 60 bayan sun amince da ita.

Yarjejeniyar ita ce kawancen kasuwanci na farko da Biritaniya za ta yi da Malaysia da Brunei, amma yayin da da ma take da yarjejeniya da sauran kasashe, tanade-tanaden wannan sabuwar yarjejeniyar ta CPTPP za ta dada kawo ci gaba, musamman ma wajen baiwa kamfanoni zabi kan yadda za su yi amfani da tanade-tanaden "dokokin asali."

Burtaniya ta yi kiyasin cewa yarjejeniyar na iya zama ta kudi har fam biliyan 2, wato kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2 da rabi a shekara na dogon lokaci.

Yarjejeniyar ta ciniki cikin 'yanci ta samo asali ne daga hadin gwiwar Trans-Pacific mai samun goyon bayan Amurka, wanda aka bunkasa a wani bangare don dakile karfin tattalin arzikin China.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG