Zababben shugaban kasar Donald Trump ya bayyana bukatarsa ta soke karin sa’a daya a lokacin hunturu da ragewa a lokacin bazara.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Juma'a, Trump ya ce jam'iyyarsa za ta yi kokarin kawo karshen wannan dabi'a idan ya koma kan karagar mulki.
Ya bayyana kari da rage tsawon lokacin rana a matsayin "abin da bai dace ba, kuma mai tsada sosai ga kasar Amurka."
Sanya karin lokacin agogo da sa’a daya a gaba a cikin hunturu, da kuma ragewa baya da sa'a guda a lokacin bazara, na da manufar kara tsawaita wuni a cikin watannin bazara, to amma kuma an daɗe ana cece-kuce da muhawara kan lamarin.
A lokuta da dama 'yan majalisar dokoki sun yi ta yunkurin kawar da wannan canjin lokaci gaba ɗaya.
Babban yunƙuri na baya-bayan nan, shi ne wani kudurin doka da aka gabatar, wanda ke bukatar barin lokacin na bazara ya dore dindindin ba tare da ragewa ba.
Dandalin Mu Tattauna