Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Mali Nijar Da Burkina-Faso Sunce Bakin Alkalami Ya Bushe Dangane Da Batun Ficewar Su Da Ga Kungiyar ECOWAS Ko CEDEAO


ECOWAS
ECOWAS

A yayin da ECOWAS ke Shirin gudanar da taro a ranar lahadi a Abuja  babban birnin tarayyar Najeriya domin tantauna makomar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wadanda wa'adin ficewar su da ga kungiyar ke cika a watan janairun shekarar 2025, kasashen sun ce bakin alkalami ya riga ya bushe.

A yayin da shugabanin kasashen yammacin Afirka ke Shirin gudanar da taro a ranar lahadi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya domin tantauna makomar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wadanda wa'adin ficewar su da ga kungiyar ke cika a watan janairun shekarar 2025, 'yan Nijar na bayyana ra'ayoyi mabambanta game da tasirin wannan taro ganin yadda gwamnatocin kasashen 3 ke ci gaba da watsi da tayin mayar da su cikin kungiyar. Masana diflomasiya na ganin akwai wuya kasashen na AES su amsa kira.

A watan Yulin da ya gabata ne taron shugabanin kasashen CEDEAO ko ECOWAS ya nada shugaban kasar Sénégal Bassirou Diomaye Faye da ya shiga tsakani, bayan da kasashen Mali. Nijar da Burkina Faso suka bada sanarwar ficewa daga kungiyar da suke zargi da kaucewa manufofin ta. Saboda haka ake kallon wannan lamari da mahimmanci.

A wata hira da manema labarai a farkon watan nan na Disamba dab da taron kasashen duniya na birnin Doha, Shugaban na Sénégal ya bayyana cewa akwai alamun nasarori a yunkurin maido da wadanan kasashen cikin kungiyar ta ECOWAS. Rahotanni dai na cewa shugabanin kasashen na ECOWAS ko CEDEAO, na fuskantar baraka a tsakanin su dangane da wannan batu inda wasu ke ganin ya kamata a karawa kasashen na AES lokaci wasun kuma na ganin a yi na’am da ficewar ta su. A nata bangare majalissar dokokin CEDEAO a sanarwar da ta fitar a baya bayan nan ta shawarci shugabanin yankin su kara wa kasashen na Mali, Nijar da Burkina Faso lokaci watakila su canza matsayin su a gaba. Masani kan sha’anin diflomasiya Mouatapha Abdoulaye na jan hankulan bangarorin akan abinda zai fi zama daidai ga talakkawan kasashen yankin.

Shugaban rikon kungiyar ta ECOWAS shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya ke bayani kan wannan dambarwa ya bayyana cewa, batun komawar Nijar Mali da Burkina Faso abu ne dake bukatar taka-tsan-tsan domin magana ce da ta jibanci harkokin al'umomin yankin baki daya. To Amma a Taron bitar da suka gudanar a ranar Juma’a a birnin Yamai, ministocin harakokin wajen kasashen AES sun jaddada cewa, bakin alkalami ya riga ya bushe kan batun ficewar kasashen uku daga kungiyar ta CEDEAO ko ECOWAS.

A saurarrin rahoton Souleiman M. Barba a sauti:

DAMBARWA KAN TARON ECOWAS .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG