Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Tuhumi Tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo


Gidan kason Scheveningen inda Mr.Gbagbo yake tsare a Netherlands.
Gidan kason Scheveningen inda Mr.Gbagbo yake tsare a Netherlands.

Babban mai shigar da kara a kotun Luis Moreno-Ocampo ya ce ba Mr.Gbagbo ne na karshen da zai bayyana a gaban kotun ba

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo sun ce za su kauracewa zabubbukan da za a yi a kasar nan gaba a wani matakin nuna rashin yarda da kai shi kotun duniya bisa zargin shi da aikata manyan laifuffukan cin mutuncin Bil Adama.

Shugabannin jam'iyyar Mr.Gbagbo ta FPI sun bayyana cewa kai shi kotun Hague da aka yi wata makarkashiya ce ta siyasa da shari'a. FPI da wasu jam'iyyu biyu masu goyon bayan Gbagbo sun ce daga yau ba sa cikin kwamitin sasanta 'yan kasar Cote d'Ivoire da dinke baraka.

Kotun duniya ta tuhumi Mr.Gbagbo da aikata manyan laifuffuka hudu na cin zarafin Bil Adama. Kotun ta bayyana shi a zaman wanda a fakaice shi ne ya aikata kisan kai da fyade da kuma sauran manyan laifuffukan da aka aikata a lokacin fadan da ya biyo bayan zabe a a farkon wannan shekara. A lokacin an kashe mutane dubu uku a kalla.

Kotun ta ce akwai wasu hujjojin da hankali zai yarda da su wadanda suka nuna cewa sojojin Mr.Gbagbo sun kai hare-hare kan fararen hular da aka zaci cewa sun goyi bayan abokin hamayyar siyasar Mr.Gbagbo.

Tashin hankali ya barke ne a kasar Cote d'Ivoire lokacin da Mr.Gbagbo ya ki mika mulki bayan zaben shugaban kasar da Alassane Ouattara ya lashe. A cikin watan afrilu aka kama Mr.Gbagbo sannan aka iza keyar shi zuwa kotun Hague a ranar Larabar da ta gabata. Ranar Litinin mai zuwa zai yi bayyanar farko a gaban kotun.

Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Mr. Laurent Gbagbo a ranar da aka kama shi a cikin watan afrilun da ya gabata
Tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Mr. Laurent Gbagbo a ranar da aka kama shi a cikin watan afrilun da ya gabata

Babban mai shigar da kara a kotun Luis Moreno-Ocampo ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike akan tashin hankalin da ya faru a kasar Cote d'Ivoire kuma ya ce ba Mr. Gbagbo ba ne karau a bayyana gaban kotu.

Moreno-Ocampo ya ce akwai shaidar da ta nuna cewa magoya bayan Gbagbo da Ouattara dukan su, sun aikata manyan laifuffukan yaki. Mr.Ouattara ya kafa kwamitin sasanta 'yan kasar Cote d'Ivoire da dinke baraka. Ya yi alkawarin tuhumar duk wanda ya aikata babban laifi a lokacin tashin hankalin.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG