Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kwaso Daruruwan 'Yan Kasar Daga Sudan


Daliban Najeriya Da Suka Samu Shiga Masar
Daliban Najeriya Da Suka Samu Shiga Masar

Daruruwan ‘yan Najeriyan da suka guje wa rikicin Sudan sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe bayan an fuskanci tasgaro wajen jigilarsu zuwa kasar Masar inda suka kwashe kwanaki a cikin Hamada cikin matsanancin yanayin rashin ruwa da abinci da rashin tabbacin abin da ka iya biyo baya.

AP

Da stsakar daren jiya Laraba, wayewar garin yau Alkhamis ne suka isa Abuja daga Misra cikin wani jirgin sojan saman Najeriya da na ‘yan kasuwa. Sama da ‘yan Najeriya 370 ne, galibin su dalibai a wannan rukunin, yayinda kimanin ‘yan kasar 2,000 suke tsakanin Sudan din da Misra kuma ake sa ran za a kwaso su cikin kwanaki masu zuwa a cewar minister ma’aikatar jinkai ta Najeriya Sadiya Umar Farouq.

Rikicin na Sudan wanda ya barke bayan kwashe watannin karuwar tashin hankali tsakanin dakarun sojan kasar ta Sudabn da kuma dakarun sojin sa kai na RSF wanda ya zuwa yanzu yayi sanadin kisan sama da mutum 550 kana ya raba dubun dubatan mutane da muhallansu. Yanayin da ya tliasta wa kasashe da dama gaggauta kwashe ‘yan kasarsu daga kasar mai fama da rikici, ko da yake miliyoyin mutane suna nan a kasar da aka yi alkawarin tsagaita wuta mai rauni.

People stand next to buses as passengers fleeing from Sudan arrive at the Argeen land port, after being evacuated from Khartoum to Abu Simbel city, at the upper reaches of the Nile in Aswan
People stand next to buses as passengers fleeing from Sudan arrive at the Argeen land port, after being evacuated from Khartoum to Abu Simbel city, at the upper reaches of the Nile in Aswan

Da sojin Najeriya da jiragen jigilar fasinjojin da suka kwaso ‘yan kasar sun girke jiragen nasu a filin jirgin saman Aswan a kasar Masar tun ranar Lahadi amma an samu jinkirin kwaso su a sanadiyyar wasu al’amuran da suke da alaka da shirye-shirye da takardun shaida a kan iyakar Misra wanda aka samu warware su a jiya Laraba kafin su taso a cewar hukumomi.

Ministar wacce ta kasance a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe tare da wasu jami’an gwamnati domin tarbar ‘yan kasar ta ce, “sun shiga halin ha’ula’i amma mun yi farin cikin ganin cewa sun iso gida lafiya ba tare da wani ya rasa ransa”.

Nigerian Evacuees from Sudan who were stranded in the deserts at the border in Egypt onboard a Nigerian Airforce craft to Nigeria
Nigerian Evacuees from Sudan who were stranded in the deserts at the border in Egypt onboard a Nigerian Airforce craft to Nigeria

An dauki bayanan duk wadanda suka dawo gida sannan daga bisani aka baiwa kowani mutum guda naira dubu dari, wato kwatankwacin dalar Amurka $216 a matsayin kudin motar da zata karasa da su gidajensu. ‘Yan uwan masu dawowan cikin farin ciki sunyi dafifi a harabar jirgin saman inda tarbe su cikin farin ciki da anashwa.

a cewar shugabar hukumar dake kula da al’amuran ‘yan Najeriya a kasashen waje Abike Dabiri-Erewa, ya zuwa yanzu, akwai ‘yan Najeriya sama da miliyan uku 3,000 000 da ke rayuwa a Sudan. Ta kara da cewa, wadannan ‘yan Najeriyar da aka kwaso ba ‘yan gudun hijira ba ne, sun dawo gida ne. Sun tafi neman illimi ne sabo da haka yanzu da suka dawo gida, kamata ya yi su koma gidajensu wajen iyayensu da iyalensu. Mun fi bada fifiko akan dalibai, mata da yara.

XS
SM
MD
LG