WASHINGTON, D.C - Wani sakon tes da Jakadan Najeriya a Masar Ambasada Nura Abba Rimi ya aikewa Muryar Amurka, ya nuna cewa ta yankin Arqeel aka shigar da daliban.
“An fi ba mata fifiko a wannan aikin shigar da daliban su 449 cikin kasar ta Masar.
“A halin da ake ciki, ana shirya daliban don kwashe su zuwa Abuja ta filin tashin jirage da ke Aswan.” Ambasada Rimi ya ce cikin sakon.
Tun bayan barkewar rikici a Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu, dubban mutane ciki har da ‘yan Najeriya suka doshi kan iyakar kasar ta Masar don kaucewa rikicin.
Sai dai hukumomin Masar sun hana su shiga kasar inda suka bukaci mutanen su nuna biza da takardun da ke nuna an tantance su daboda dalilai na tsaro.
Kwanan tawagar daliban Najeriya hudu akan iyakar ta Masar kafin ba su samu wannan dama a ranar Talata.
Rikicin na Sudan ya kaure ne tsakanin dakarun kasar da ke karkashin Janar Abdel Fatah El Burhan da na rundunar RSF ta musamman da ke karkashin Janar Mohamed Hamdan Dagalo.
Daruruwan mutane sun mutu kana dubbai sun jikkata yayin da jama’a da dama suka fice daga birnin Khartoum mafi akasari jami’an diflomasiyyan kasashen duniya da dalibai.