Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Tura Jirgin Sojin Sama Don Kwaso 'Yan Kasarta Da Suka Makale A Sudan


Daliban Najeriya a Sudan yayin da ake shirin kwashe su zuwa kan iyakar Masar (Twitter/Abike Dabiri Erewa)
Daliban Najeriya a Sudan yayin da ake shirin kwashe su zuwa kan iyakar Masar (Twitter/Abike Dabiri Erewa)

Tun a ranar Alhamis 27 ga watan Afrilu ‘yan Najeriyar suka isa Aswan, yankin na Masar da ya hada iyaka da Sudan.

Jirgin sojin saman Najeriya, ya kama hanyarsa ta zuwa Masar domin kwaso 'yan kasar da suka makale a Sudan.

A tsakiyar makon da ya gabata aka kwaso 'yan Najeriyar daga Sudan wadanda galibinsu dalibai ne aka kai su kan iyakar Masar.

Sai dai rahotanni daga kan iyakar Sudan da Masar na nuni da cewa har yanzu mutum sama da 7,000 ciki har da ‘yan Najeriya sun kasa shiga kasar ta Masar bayan da hukumomi suka hana su ketarawa.

Mutanen sun tserewa rikicin Sudan ne, inda suka nufi kasar ta Masar domin gwamnatocinsu su kwashe su daga kasar.

"NAF C-130 na shirin zuwa Masar don debo 'yan Najeriya da suka makale a Sudan." Hukumar NIDCOM da ke kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta rubuta hade da wani bidiyo da ta wallafa a shafin Twitter ta ce.

An ga jami'ai suna ta loda kayan abinci da ruwa a cikin jirgin kafin ya tashi daga Najeriyar.

Tun a ranar 15 ga watan Afrilu Sudan ta fada cikin rikici bayan da yaki ya kaure tsakanin rundunar sojin kasar da mayakan sa-kai na RSF.

A ranar Juma’a hukumar ta NIDCOM, ta ce ofishin jakadancin Najeriya na kokarin neman maslaha da hukumomin Masar don a ba ‘yan Najeriyar dama su shiga kasar.

Tun a ranar Alhamis 27 ga watan Afrilu ‘yan Najeriyar suka isa Aswan, yankin na Masar da ya hada iyaka da Sudan.

Gabanin zuwansu yankin, an dan samu tsaiko inda direbobin bas din da suka kwaso su daga Sudan, suka yi bore suka tsaya a tsakiyar a Sahara saboda ba a cewarsu, ba a biya su kudadensu ba.

Amma daga baya, hukumar ta NIDCOM ta ce an sasanta lamarin.

XS
SM
MD
LG