Kowane dan’adam kan bukaci abu mai sanyi, musamman idan mutun yayi wani aiki da yake sa jin zafi, da yawa idan mutane sunji zafi, zasu so su fara da ruwan sanyi ko wani abu da zai sanyaya musu jikin su.
Taron wasu manazarta wanda ya bayyanar da irin illoli, da abubuwa masu sanyi kan haifar ga lafiyar dan’adam. Yanayin zafin jikin mutun, da ya kamata a samu mutun cikin shi a kowane lokaci shine, ma’aunin 98.6 na digiri, a duk lokacin da mutun ya wuce hakan sai a bincike lafiyar shi.
Masanan sun tabbatar da cewar, yawan shan ruwan sanyi, na nakasa zuciya, da na’urar da kan sarrafa abinci a cikin cikin dan’adam. Haka abu mai sanyi na wargaza yanayin zafin jikin mutun.
A duk lokacin da mutun ya sha abu mai sanyi, yana iya samun maganin matsalar da tasa shi shan abun, na kankanin lokaci, wanda a bangare daya kuwa yana iya haifar da matsala a tsawon lokaci.
Shan abu mai sanyi kan haifar da rashin sarrafa abinci da mutun yaci, cikin lokaci da ya kamata, yana iya haifar da cutar makoshi, haka mutun kan iya rasa wasu sinadaran gina jiki. Domin kuwa a duk lokacin da zafin jikin mutun ya sauka kasa sai mutun ya samu zafin da yake bukata kamin jikin shi yayi aiki yadda ya kamata.
Don haka akwai bukatar mutane su, dinga kwatantawa wajen sha ko kusantar abu da ke dauke da sanyi, da zai haifar da rashin lafiya ga rayuwar su, musamman matasa, da hakan zai tambaye su a lokacin tsufa.