Mun nazarci wasu kadan daga cikin dalilan da suke sa mawaka, a kasar Amurka tsiyacewa shekaru kadan bayan fara sana’ar waka. Wanda muka gano wasu daga ciki. Mawaki Sean Kingston, ya ci bashi da yakai dallar Amurka milliyan dari biyu $200M, wanda rashin biyan bashin yasa har aka kwace motocin da yake hawa da duk wani abu da ya mallaka.
Haka shima fitaccen mai wasan barkwancin nan Chris Tucker, yayi zanba cikin aminci, na rashin biyan haraji da ya kai dallar Amurka milliyan goma sha hudu $14M, yanzu haka dai yana biyan wadannan kudaden da zasu iya daukar shi lokaci maitsawo kamin ya gama biya.
Mawaki Khujoof Goodie Bob, ya tara abun duniya, amma a lokacin da duniya ta juya mishi kuwa, sai gashi an korashi da matar shi da ‘ya’yan shi hudu, daga gidan da suke, ya tsiyace a wani lokaci abun da suka rage a asusun banki shi basu kai $300, ba.
Fitaccen mawaki Nelly, ya nemi shiga cikin sarkakiya, inda ya kashe mafi yawan kudin shi a wajen ca-ca, kana da basusuka da ake binshi, amma yayi dubara wanda ya kokarta wajen gujema wannan rayuwar, yanzu haka dai yana da kudi da suka kai dallar Amurka milliyan sittin $60M. Itama mawaki Lauryn Hill, ta fada cikin ramin gujema biyan haraji, wanda hakan ya sata rasa kaso mafi yawa a cikin dukiyar da ta mallaka.
Mawaki Ja Rule, bayan kwashe wasu watannin kadan da yayi a gidan yari, bisa dalilin rashin biyan haraji, yanzu haka dai ana bin shi bashi da yakai dallar Amurka milliyan daya. Mawaki Bustarain shima ya kwashi wadda rafi cikin shi. Mafi aksarin mutane da suke samun manyan kudi a kasashen da suka cigaba, suna biyan haraji da yayi yawa.