Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabbatar Da Sahihancin Labarai Dake Kan Hanyoyin Sadarwa


Kamfanin sadarwan nan mai fitatcen shafin bincike na yanar gizo Google, ya fitar da sanarwar zai fara saka wata alama a duk labaransa don tabbatar da cewa suna da sahihanci.

Wanda yanzu haka ake ganin lokaci ne da Facebook ya kamata ya dauki wannan batu na tabbatar da sahihancin labarai da muhimmanci. Kasancewar Facebook ya zamanto wata hanya da yawancin mutane ke samun labaransu, haka kuma dandali ne da masu amfani da shi ke iya samun duk labaran da suke so.

Hakan yasa nauyi ya rataya kan Facebook na ganin yayi gyara a harkar isarwa da mutane labaru, ta hanyar tabbatar da sahihancinsa da kuma inda labarin ya samo asali, domin gujewa labarum karya da almara.

Tun lokacin da Facebook ya kori editan dake tace labaru a shafinsa, ya koma dogaro ga manhaja ta rika aikawa mutane labarai masu dumi dumi, tun wannan lokaci labarai masara sahihanci ke yawo akai akai a shafin yanar gizo.

A watan Satumba ne Facebook yayi ikirarin samar da wata sabuwar fasaha da zata ke tace labarai marasa kyau cikin jerin labaranta masu dumi dumi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00

XS
SM
MD
LG