Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kundin Tarihin Duniya: Kyakyawar Budurwa Da Gemu Kamar Namiji!


Harnaam Kaur
Harnaam Kaur

A wani sabon rahoton hukumar ajiyar abubuwan tarihi a duniya “Guinness World Records” a bana sun bayyanar da wata matashiya mai shekaru ashirin da hudu 24, a duniya, a matsayin waddda ta lashe kambun shekarar 2017.

Harnaam Kaur, ‘yar asalin kasar Birtaniya, wadda take da yawan gashin fuska "Gemu" kamar namiji. Ta bayyanar da labarin ta, a matsayin wani abun da ta sha wahala, domin kuwa idan aka ganta da gemu da gashin baki, sai a dinga tsokalanta. Haka yasa ta shiga cikin damuwa, amma daga bisani ta dauki cewar, wannan wata baiwa ce da Allah yayi mata.

Tun tana ‘yar shekara goma sha biyu 12, ta fara gemu, a wannan lokacin ne aka duba lafiyar ta, aka gano cewar, jikin ta yana dauke da wani sinadari dake hana fitowar gashi a jikin mata, ita nata yana da karfi, don haka gashi zai dinga fitowa a jikin ta kamar namiji.

Tun dai a wannan lokacin ne ta daina yanke gashin fuskar ta, yanzu haka dai gashin nata yakai tsawon zira’I ko a ce inci shida 6. A yayin wani bukin nuna kawar kaya, Harnaam, ta gabatar da kanta a matsayin mace da tafi yawan gashi a tsakanin mata, hakan ya jawo hankalin mutane da dama a kasar Ingila.

Ta bayyanar da cewar, wannan baiwace da ga Allah, don haka kada wani ko wata su raina irin baiwar da Allah yayi musu a rayuwa. Hasalima sai su gode mishi, domin yanzu gashi ta shiga cikin tarihin duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG