A wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja, Ministan Albarkatun Ruwan Najeriya, Injiniya Sulaiman Husaini Adamu, yace dubban mutane ne ke mutuwa saboda cututtukan da suke dauka bisa dalilan rashin wanke hannu da sabulu.
Minista yace bincike ya nuna cewa idan mutane suka dukufa suna wanke hannunsu a lokacin da ya kamata, to zai rage cututtuka sosai. An yi lissafi, kamar a Najeriya mutanen dake mutuwa a sanadiyyar cututtuka dake da nasabar rashin wanke hannu dai dai yake da faduwar babban jirgin sama yana kashe mutune a rana.
Ma’aikatar Albarkatun Ruwa na ‘daukar matakan wayar da kawunan mutane, inda aka mayar da hankali wajen koyarwa kananan yara ‘yan makaranta muhimmancin wanke hannu da sabulu, domin su fara wannan ‘dabi’a tun suna yara.
Shima jami’in hukumar kananan yara ta UNICEF ta MDD a Najeriya, Mr. Kalal Ladar, yace “Yara masu yawan gaske ne ke rasa rayukansu saboda gudawa da kazanta ke haddasawa da kuma rashin wanke hannu, abin da ba wani kudi yake bukata ba kafin ayi shi. Abu ne mai sauki da yafi rigakafi muhimmanci.