Kamfanin sada zumunci na Facebook na shirin gwajin wata sabuwar fasahar wireless ta yin amfani da kananan jirage masara matuki wato drones.
Facebook ya shirya wannan gwaji ne a hedikwatar kamfanin dake Silicon Valley, ta hanyar tayar da wannan karamin jirgi mai dauke fasahar wireless din har tsawon kafa 400 a sararin samaniya, cikin ‘yan watanni masu zuwa.
Wasu bayanai na nuni da cewa Facebook ya nemi izinin wannan gwaji daga hukumar dake kula da harkokin sadarwa ta Amurka FCC, kan cewa zaiyi gwajin mita 2.4 ta rediyo.
Bayanan na nuna cewa dalilin wannan gwaji kuwa shine don gwada wata sabuwar fasahar sadarwa, ta amfani da matsakaicin zango a sararin samaniya. Kamfanin dai yace yana son gudanar da wannan gwaji tsakanin watan Oktoba da watan Afrilu.
Facebook dai na kera wani jirgin drone wanda zai ke amfani da hasken rana, kuma tayi amfani da shi wajen rarraba yanar gizo a wasu sassa na duniya. Jirgin dai na da girma sosai, an kuma tsara shi yadda zai iya kaiwa nisan ‘kafa Dubu 60 a sararin samaniya inda zai ke tashi duk watanni Uku. Facebook dai na gwajin wadannan jirage a jihar Arizona dake Amurka.