A yau talata ma'aikatar harkokin wajen Japan ta ce za a yi amfani da wani bangare na wannan kudin agajin domin karfafa rundunar AFISMA wadda kasashen Afirka suke jagoranci a kasar Mali, wadda kuma take taimakawa wajen sake kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan tawaye masu kishin Islama.
Har ila yau ta ce wannan agaji zai taimaka wajen karfafa mulki, da kyautata tsaro da rage talauci a yankin na Sahel, yanki mai yawan fama da karancin ruwan sama wanda ya kamo daga Senegal a yamma har zuwa kasar Chadi a gabas.
Da ma dai Japan ta ba yankin agajin dala miliyan 63 a cikin shekara guda da ta shige. Har yanzu kasar ta Japan tana jimami a bayan da aka kashe 'yan kasarta su 10 a harin da wasu masu kishin Islama suka kai kan wata masana'antar gas ta kasar Aljeriya a watan nan.