Wakiliyar Muryar Amurka, Anne Look, ta ce a bisa dukkan alamu tankokin sun doshi inda sojojin Faransa suka ja daga ne. Faransa tana kara yawan dakarunta a kasar Mali, inda ta aike da tankoki da motocin yaki masu sulke, yayin da take ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan tawaye daga sama.
Look ta ce a jiya talata, motocin yaki guda 100 na Faransa sun isa Mali daga Ivory Coast makwabciyarta, kuma karin sojoji sun doshi can daga Chadi da Faransa.
A halin da ake ciki, shaidu sun ce jiragen yakin Faransa sun yi luguden wuta a kan garin Diabaly cikin dare, ‘yan sa’o’i kadan a bayan da mayaka masu nkishin Islama suka kama wannan gari mai tazarar kilomita 400 a arewa da birnin Bamako. Mazauna garin sun ce har yanzu ‘yan tawayen ne ke rike da garin.
Jami’an tsaro na Faransa sun ce sannu kan hankali, yawan dakarunsu a Mali zai karu zuwa dubu 2 da 500. Najeriya kuma ta ce a yau laraba sojojinta na farko zasu sauka a kasar Mali, a wani bangare na rundunar sojojin kasashen Afirka ta Yamma da zasu taimaka ma sojojin gwamnatin Mali wajen kwato arewacin kasar.
Shugaba Francois Hollande na Faransa ya fada jiya talata a Dubai cewa sojojin faransa zasu zauna a Mali har sai an samu kwanciyar hankali.
Tsagera masu alaka da kungiyar al-Qa’ida sun kwace arewacin Mali a bayan da wasu bijirarrun sojoji suka hambarar da gwamnatin kasar a watan Maris, suka haddasa yanayi na rashin hukuma na wani dan lokaci a kasar.