Rahotanni sun ambaci wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suka bukaci da kada a bayyana sunayensu, su na fadin cewa watakila za a kafa wannan sansani ne a Jamhuriyar Nijar.
Suka ce idan har akia amince da wannan shiri, sansanin zai iya kunsar sojojin Amurka guda 300.
Nijar tana makwabtaka da kasar Mali inda sojojin Faransa da na Mali suke gwabzawa da masu kishin Islama.
Jaridar “New York Times” wadda tafara ba da wannan rahoto, ta ambaci wani jami’in sojan Amurka, yana cewa babban makasudin sansanin shi ne rikicin da ake yi a Mali, amma kuma sansanin zai yi amfani ga ayyukan leken asiri na Amurka a fadin yankin baki dayansa.
Amurka tana da sansanin soja kwaya daya ne tak na dindindin a nahiyar Afirka, wanda ke kasar Djibouti, mai tazarar kilomita dubu 5 daga kasar Mali.