Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Tana Son Sojojin Afirka Su Yi Jagoranci


Wanbi sojan Faransa yana gadi a sansanin mayakan sama na Mali inda mayakan saman Faransa suka kafa sansani
Wanbi sojan Faransa yana gadi a sansanin mayakan sama na Mali inda mayakan saman Faransa suka kafa sansani

Ministan harkokin wajen Faransa ya nemi hakan a taron kolin gaggawa na shugabannin kasashen Afirka ta Yamma a Abidjan, kan rikicin Mali.

Ministan harkokin wajen Faransa, yace lokaci yayi da dakarun Afirka zasu karbi jagorancin yakin fatattakar ‘yan tawaye masu kishin Islama daga yankin arewacin kasar Mali.

Laurent Fabius yana magana ne a wajen taron kolin gaggawa da shugabannin kasashen Afirka ta Yamma suka yi a Abidjan, cibiyar kasuwanci ta kasar Cote D’Ivoire, inda suka tattauna yadda zasu tura karin sojoji zuwa Mali domin tallafawa sojojin Faransa a wannan fada.

Ana sa ran cewa kasashe makwabta zasu tura sojoji akalla dubu 3 zuwa Mali, a bayan da Faransa ta tsoma hannunta mako guda da ya shige domin jan burki ma ‘yan tawaye masu kishin Islama dake rike da arewacin kasar a lokacin da suka yi yunkurin kutsawa kudu.

A ranar jumma’a, jami’ai a kasar ta Mali sun ce sojojin gwamnati wadanda dakarun faransa ke marawa baya sun kwace garin Diabaly, suka fatattaki masu kishin Islama da suka kwace garin ranar litinin. Tun kafin nan, sojojin Mali sun bayyana cewa sun kwace garin Konna dake gabas da nan daga hannun ‘yan tawayen.

Jami’an Faransa sun ce a yanzu haka akwai sojojinsu dubu 1 da 800 a Mali, kuma yawansu zai karu zuwa dubu 2 da 500 a cikin ‘yan kwanakin dake tafe. Faransa ta ce sojojinta zasu ci gaba da zama a kasar har sai an samu kwanciyar hankali.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG