Mazauna garin Hombori da kuma jami’an tsaro sun ce sojojin Faransa da na Mali sun kara da ‘yan tawaye jiya jumma’a a garin, mai tazarar kilomita 250 daga birnin Gao.
A halin da ake ciki, jami’an yanki sun ce ‘yan tawayen sun tayar da bam a kan wata muhimmiyar gada dake kusa da bakin iyakar kasar ta Mali da Jamhuriyar Nijar.
An shiga mako na uku ke nan yanzu da farmakin da dakarun kasasahen waje suka kaddamar karkashin jagorancin Faransa a kan ‘yan tawaye masu kishin Islama da suka kwace akasarin yankunan arewacin Mali.
Wakilin Muryar Amurka Idrissa Fall dake Mali yace sojojin Faransa da na Mali sun dirkaki wuraren da ‘yan tawayen suka yi tunga.
Sannu a hankali za a maye gurbin sojojin Faransa da na kasashen Afirka ta Yamma wadanda suka fara isa kasar ta Mali a yanzu haka.
A halin da ake ciki, daya daga cikin kungiyoyin kishin Islama dake mamaye da sassan arewacin kasar ta Mali ta rabe gida biyu. A ranar alhamis ne wasu ‘ya’yan kungiyar Ansar Dine suka ce sun balle sun kafa kungiyar Islama ta Azawad. Sabuwar kungiyar ta bayyana aniyarta ta shiga tattaunawa da nufin warware rikicin kasar Mali.