Ministan Harkokin Tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya ce ‘yan tawayen sun kwace garin Diabaly, mai tazarar kilomita 400 a arewa da birnin Bamako, bayan wani kazamin fada da dakarun Mali.
To amman ya ce matakan sojan da Faransa take dauka a kasar Mali su na gudana kamar yadda Shugaba Francois Hollande ya tsara.
Wakiliyar Muryar Amurka Anne Look, tana birnin Bamako daga inda ta bayar da rahoton cewa sojojin Mali na shirin tura dakarunsu zuwa garin na Diabaly a wani yunkurin fatattakar ‘yan bindigar, wadanda aka ce su na dauke da muggan makamai.
Kasar Faransa ta girke sojojinta a wannan kasar ta Yammacin Afirka ranar Jumma’a, a daidai lokacin da ‘yan tawayen da ke arewa su ka yi shirin kwace wuraren da ke karkashin ikon gwamnati.
Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya, Gerard Araud, ya ce Faransa ta yanke shawarar tallafa wa Mali ne saboda ta damu cewa ‘yan tawayen na iya kwace babban birnin kasar.