Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Faransa Sun Sake Luguden Wuta A Mali


Jirgin saman yakin Faransa na shirin tashi daga sansanin Kossei a N'Djamena kasar Chadi, Jumma'a 11 Janairu 2013
Jirgin saman yakin Faransa na shirin tashi daga sansanin Kossei a N'Djamena kasar Chadi, Jumma'a 11 Janairu 2013

Nijar da Burkina Faso su na shirin tura sojoji dari biyar kowaccensu domin haduwa da na Najeriya da Senegal wadanda tuni suka isa kasar ta Mali

Jiragen saman yakin Faransa, sun sake yin luguden wuta a rana ta biyu a jere jiya asabar kan ‘yan tawaye masu kishin Islama a kasar Mali, a daidai lokacin da kungiyar tarayyar tattalin arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta bayar da iznin girka karin sojojin kasashen waje nan take a Mali.

Jami’ai suka ce dakarun Faransa, sun fatattaki ‘yan tawaye daga garin Konna, ta hanyar kai musu hare-hare daga sama, da kuma ta kasa. Kama wannan gari na Konna dake arewa maso gabas da Bamako, babban birnin kasar, da ‘yan tawaye suka yi a cikin mako, ya sanya su cikin sukunin iya kama birnin Mopti dake kusa da nan, birnin da shi ne mafi arewaci dake hannun gwamnatin Mali.

Wani dan jarida a Mali, ya fadawa sasahen Faransanci na VOA cewa an kashe ‘yan tawayen Islama da dama a fadan na Konna. Har ila yau dan jaridar yace ya zuwa daren asabar, garin yana hannun sojojin gwamnatin Mali, yayin da mayakan masu kishin addini dake gudu daga garin suka buya a garuruwan Bore da Douentza.

Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian ya fada jiya asabar cewa an harbo wani jirgin helkwafta na Faransa, kuma matukinsa ya mutu a lokacin da ake kai hare-hare ta sama a kan garin Konna.

Tsageran kungiyar Ansar Dine masu alaka da al-Qa’ida sun mayarda martani ga hare-haren ta hanyar yin barazanar kai hare-haren daukar fansa a kan Faransa, abinda ya sa shugaba Francois Hollande ya bayarda umurnin kara tsaurin matakan tsaro a duk fadin kasarsa. Har ila yau, hukumomin Faransa sun shawarci dukkan Faransawa dake Mali da su bar kasar na wani dan lokaci.

A halin da ake ciki, Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta bayar da iznin girka sojojin Afirka nan take a kasar Mali. A jiya asabar, kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun bayar da sanarwar cewa kowaccensu zata tura sojoji dari biyar.

Tuni, Najeriya da Senegal suka tura tallafin sojoji zuwa kasar ta Mali.

A London, firayim minista David Cameron na Britaniya ya bayarda umurnin da a kai daukin kayan aiki, ciki har da jiragen saman jigilar kaya na Britaniya, domin tallafawa matakan sojan da Faransa take dauka a kasar Mali.
XS
SM
MD
LG