Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin wakili na musamanman Mista Jett Radebe da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya aika a fadarsa dake Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi suka da kakkausan lafazi a kan irin kiyayya da musgunawar da ake yi wa ‘yan Nigeria a kasar Africa ta kudu, wadda Najeriya ta taimaka ma ta ainun a zamanin wariyar launin fata.
Bayan ya rantsar da sabbin ministocinsa, shugaba Buhari ya ce su fi maida hanakali akan maufofin gwamnatinsa guda 4.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu buhari ya bayyana irin mummunar satar arzikin da dukiyoyin da ake yiwa kasashen Afirka zuwa kasashen ketare.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan kudirin dokar taimakon juna na kasa da kasa, wajen samar da bayanan sirri kan manyan laifuffuka da suka hada cin hancin da rashawa.
Yau ne sabuwar ranar dimokradiyya a Najeriya, ranar da za’ayi bukukuwan rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a wa’adi na biyu bayan da aka rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu da ya gabata.
A ziyarar da Yan majalissun Tarayyar Najeriya suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa ya nuna rashin jin dadin goyon bayan da basu bashi ba a wa'adin mulkinsa na farko.
Bayan da hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta bayar da sakamakon zaben da ke nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ‘yan Najeriya suka sake zaba da kuri’un da suka haura miliyan 15.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa a Abuja tare da wasu tare da wasu kusoshin jam’iyarsa ta APC mai mulkin kasar, inda shugaban kasar ya ya gargadi yan majalisar da suyi kampe a kan ‘ka’ida da manufa mai kyau ba tare da ‘batanci ko cin zarafin kowa ba.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnoni guda takwas karkashin jagorancin gwamnan Zamfara, domin neman hanyar warware matsalolin da suka shafi zabukan fitar da ‘yan takara a jam’iyyar APC.
Sabon direkta Janar din hukumar leken asirin Najeriya DSS Mr Mathew Seyeifa ya gana da manema labarun Najeriya inda ya bayyana matakan da zai dauka na inganta aikin hukumar.
Yanzu haka wannan tafiyar ta janyo cece-ku-ce tsakanin ‘yan siyasar kasar dake zargin cewa batun lafiya ne zai kai shugaba Buhari Ingila.
Kasar Netherlands za ta taimakawa Najeriya wajen farfado da tafkin Chadi da kuma dakile sauran ta’addancin da kungiyar Boko Haram ke yi a arewacin kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawa ta musamman da kungiyar Kiristoci ta Najeriya daga Jihohin Arewa 19 ciki har da Abuja, inda suka koka da yawan matsalolin tsaro da yawan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a sassa dabam-dabam na Najeriya.
An yi ganawa ta musamman a fadar gwamnatin tarayya tsakanin shugaban Najeriya da shugabannin Majalisun ‘kasa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba zata mayar da wani martani ba a yanzu dangane da sharudan da Majalisar ‘kasa ta mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Domin Kari