Ga dukkan alamu, kudirin dokar da Shugaba Buhari ya bada sanarwar zai fara amfani da ita domin kwace dukiyoyi da kadarori na wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa na dan karamin lokaci kafin kotu ta tabbatar da laifinsu yana ci gaba da kawo cece-kuce tsakanin 'yan siyasa da kuma wadansu lauyoyin masu rajin kare hakkin bil adama da bin dokokin dimokradiyya.
Buhari ya rattaba hannun ne domin kokarin tabbatar da cewa an samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa, a yayin da wasu 'yan siyasa ke ganin cewa yana son ya yi amfani da wannan dokar ne wurin kuntatawa masu adawa da shi ko kuma wadanda ba su ba shi goyon baya.
Kakakin fadar gwamnatin tarayya, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, lallai wasu 'yan siyasa ko lauyoyi ba su fahimci wannan kudirin dokar ba.
"Abun da wannan doka ta ke son ta yi shine, jingine duk dukiya da ake zargin cewa haramtacciya ce, doka ta bada iko ga shugaban kasa ya jingine na wucin gadi har sai an gama bincike ko shari'a," inji Shehu.
Garba ya bayyana cewa dalilin da yasa aka dauki wannan mataki shi ne, sau da yawa idan aka ce ga zargi ana yi kan abin da wani ya sata, kafin an ankara an wawushe dukiyarna, an fitar da ita kasashen waje ko ta salwanta.
"Bukatar gwamnati shi ne, kada a rasa abin da ake nema. In ka diba ba naka ba ne, to dukiyarnan a dawowa jama'a da ita," inji Shehu
Game da batun cewa kotu ce kadai za ta iya bada wannan umarnin ya zama doka ba shugaban kasa, Shehu ya ce shi wannan dokar iyakacinta shugaba ya bada umarni ga atoni janar ya je gaban mai shari'a ya nemi izinin dakatar da amfani da dukiya har sai an gama bincike ko shari'a.
Haka zalika, ya ce cikas da hukumomin EFCC da ICPC ke samu akan aikinsu shi yasa Buhari ya fito da wannan kudirin domin a gaggauta kuma a samu nasara akan cin hanci da rashawa.
Sai dai wani lauya kuma masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, Barista
Abdulhamid Muhammed ya bayyana cewa babu dalilin yin wannan kudirin dokar saboda hukumar EFCC da ICPC suna nan suna aikinsu kuma doka akan haka ta sani ba kuma zai kawo matsala ba.
"Ba za a zo a yi maka karan tsaye akan abin da ka mallaka ba, a ce shi kenan an kwace. Sai in wani ya zo ya kawo kuka ko kuma su jami'an gwamnatin da ke aiki a wadannan hukumomin suka fara bincike ka zo ka yi musu bayani."
Ya ce wannan kudirin ya saba doka saboda dokokin da ke cewa sai an gayyaceka, ka zauna da hukumomin bincike, sun yi bincike don tabbatar da yadda lamarin yake. In bincike nuna sannan a nemi izinin kotu kafin a dauki wannan matakin dakatar da amfani da dukiya.
Saurari rohoton Umar Faruk
Facebook Forum