Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gana Da Kungiyar Kiristocin Najeriya


Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kiristoci ta Najeriya na jihohin Arewa da Abuja
Buhari ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kiristoci ta Najeriya na jihohin Arewa da Abuja

​​Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawa ta musamman da kungiyar Kiristoci ta Najeriya daga Jihohin Arewa 19 ciki har da Abuja, inda suka koka da yawan matsalolin tsaro da yawan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a sassa dabam-dabam na Najeriya.

A lokacin da ya ke karbar wannan ziyarar ta su, Shugaban ya yi juyayi da nuna bakin cikinsa da zarge-zarge da wadansu 'yan Najeriya wadanda ya kira makiya zaman lafiya da cewa, wai a matsayinsa na Shugaban Kasa yana da hannu akan kashe-kashen da ake yi a wadansu sassa na Najeriya domin yana bafillatani.

Ya bada misali cewar, a 2001 a jihar Filato, an yi tashin hankalin da aka kashe daruruwan mutane, ta kai ga kafa dokar ta baci har aka cire gwamna aka nada wani na riko domin samar da zaman lafiya a wannan yankin.

A saboda haka ya ke cewa, wannan irin tashin hankalin da ake samu a sassa dabam-dabam a arewacin kasar, ba bakon abu ba ne. Amma ya zafafa saboda zarge-zarge da wadansu mutane ke yi cewa wai akwai hannu na siyasa ko na gwamnati a cikin wannan tashin hankali.

Shugaban ya yi amfani da wannan ziyarar wurin tabbatarwa 'yan Najeriya cewa a matsayinsa na shugaba, akan hakkinsa ne a kowane dan kasa da dukiyarsa, da wanda ya zabe shi da wanda bai zabeshi ba, da dan yankinsa da wanda ba ya yankinsa, cewa hakkinsa ne ya kawo zaman lafiya a wannan sassan.

“Mu taru mu kunyata wadanda ke rura wutar rikicin kabila dana addini domin cin ribar kashin kamsu a siyasance wadda hakan mai dorewa ba ne a garesu. Wannan kasar ta kowa ce kama daga Kirista da Musulmi har ma da ‘yan gargajiya,” inji Buhari.

Dangane da zuwansu wajen Buhari, shugaban kungiyar CAN na arewacin Najeriya, Reverend Yakubu Pam ya ce gani suka yi ya kamata su zo domin yi masa magana ya kara daukan matakan inganta harkar tsaro.

"Dole mu zo mu yi ma shi magana domin ya ankarar da shugabannin tsaro, sojoji da 'yan sanda kuma na gasganta zai yi," inji Pam. Yace suna sa ran cewa sauran shugabannin addinai za su tashi tsaye domin ganin wannan fitinar ta zo karshe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG