Kudirin dai ya kunshi samun hadin kai ko kuma taimakon juna tsakanin kasashe bisa yaki da manyan laifuffuka, wannan doka ce da kasashe zasu dunga taimakawa junan su wajen samar da bayanai akan duk wadanda suke aikata mugayen laifuffuka kamar su cin hanci da rashawa.
Dokar dai zata tabbatar da nemo inda suke da nuna inda suka yi ajiyar kudadensu, da kaddaorri da suka mallaka kamar su gidaje da sauran su. Kasashen zasu taimaka wajen dakile amfani da irin wannan dukiyoyi da aka same su wajen cin hanci da rashawa ko zamba, sannan arike dukiyoyin da hana duk wadanda suka saci kudin amfani da kudin Kuma a tabbatar da andawo wa da kasar da take da wannan kudaden kudiyar ta.
Sannan kuma a tabbatar da an bada bayanan sirri akan duk wani wanda ake zargi sa da cin hanci da rashawa domin a gurfanar dasu.
Saurari Rahoton Umar Farouk Musa Cikin Sauti.
Facebook Forum