A jamhuriyar Nijer kungiyar ''SAMAN, ta alkalan shari’a, ta nuna bacin rai akan yadda masu fada a ji a kasar ke kin mutunta hukuncin kotu, haka ya sa kungiyar ta bukaci shugaban kasa Mahamadou Issouhou, ya tsawata wa masu wannan muguwar dabi’a dake barazana ga dimokradiya.
Alhazan jamhuriyar Nijer sun fara nuna kosawarsu kan jiran jirgin da zai mayarda su gida bayan kammala aikin hajjin bana. Daya daga cikin wakilan tsare tasren hajjin kasar ta Nijer Alhaji Bukari Zilli ya sanar da cewa an gama komai na soma dakon alhazan daga gobe 6 ga watan Satumba zuwa Nijer.
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifyar wani dan Majalisar Dokoki a kauyen Gueskerou dake yankin Diffa, suna neman a biya su kudin fansa.
Jama’ar jamhuriyar Nijer sun nuna juyayi akan rasuwar tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Anan wanda Allah ya yiwa cikawa a shekaranjiya asabar. Suna masu yiwa marigayin kyaukyawar shaida saboda gudunmuwar da ya baya a fannoni da dama.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da harkar abinci a duniya wadanda suka hada da WFP da FAO da IFAD sun amince zasu tallafawa jamhuriyar Nijar da Dala Biliyan 1.2 wanda kasar ke bukata domin gudanar da ayyukan raya karkara a tsawon shekaru uku masu zuwa.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da harkar cimaka da suka hada da WFP da FAO da IFAD sun amince zasu tallafawa jamhuriyar Nijar da Dala Biliyan 1.2 da kasar ke bukata, domin gudanar da aiyukan raya karkara a tsawon shekaru uku masu zuwa.
Hukumomin kiwon lafiyar al’ummar a Janhuriyar Nijer sun bada sanarwar mutuwar mutane 26 daga cikin mutane kusan 1500 da suka kamu da cutar amai da gudawa a gundumar Madarunfa dake yankin Maradi.
Ya yin da al’umar musulmi ke shirin gudanar da shagulgulan babbar sallah, kasuwannin dabobi a birnin Yamai na jamhuriyar na fama da rashin ciniki.
Jam'iyar Adawa na ci gaba da cece kuce akan Yarjejeniyar gyara fadar shugaban jamhuriyar Nijar da wani kamfanin Indonesia zaiyi
Jam’iyar CDS Rahama ta bada sanarwar korar wasu makarrabanta wadanda tace suna yin zagon kasa da nufin haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yayanta sai dai wadanda matakin ya shafa sun ce ba za ta sabu ba.
An kawo karshen shari’ar da aka dade ana yi tsakanin kasar Nijar da kamfanin Birtaniya dake yin Fasfo na Africard.
Hotunan gidajen da suka ruguje a wani kauye dake kewayen Yamai a Jamhuriyar Nijer sakamakon ambaliyar ruwa.
A jamhuriyar Nijar matasan kirista na Majami’ar Evangelique sun fara gudanar da taronsu na kasa karo na 45 a birnin Yamai
Masu rajin kare demokaradiya a jamhuriyar Nijar sun maida martani bayan da shugaban kasa Mahamadou Issouhou ya dora alhakin koma bayan ilimi a wuyan dalibai da malaman kasar.
A Janhuriyar Nijer kungiyoyin nakasassu sun yi zaman dirshe a yau da safe a harabar ma’aikatar ministar jin dadin al’umma da nufin nuna rashin jin dadinsu akan abinda suka kira tauye hakkokin su.
Hukumar tace labarai a Nijar CSC ta maida martani bayan da kungiyoyin ‘yan jarida suka zargeta ta nuna halin ko in kula akan matakin rufe wasu kafafe masu zaman kansu da ma’aikatar haraji ta kaddamar a ‘yan kwanakin nan saboda rashin biyan haraji.
A Jamhuriyar Nijer, jarabawar ajin karshe a makarantun share fagen shiga jami’a da aka gudanar a tsakiyar watan nan na Yuli ta bar baya da kura bayan da wata cibiyar jarabawa ta bayyana sunan wani dalibin da ya rasu a jerin wadanda suka yi nasara.
Shugabannin masu fafutukar da kotun birnin Yamai ta sallama daga kurkuku a ranar Talatar da ta gabata, sun sake jaddada anniyar ci gaba da gwagwarmaya har sai sun sauyawa hukumomin kasar ra’ayi a game da dokar harajin 2018 saboda a cewarsu talakawa na dandana kuda a sanadiyyarta.
Kotun birnin Nyamai ta umurci hukumomin jamhuriyar nijer su sallami jami’an fafitikar da suka garkame a gidajen yarin yankin Tilabery tun a ranar 25 ga watan Maris saboda zarginsu da gudanar da zanga zanga ba da izinin hukuma ba
Domin Kari