Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Za Ta Tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa


Gidaje Sun Ruguje Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Yamai, Nijar
Gidaje Sun Ruguje Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Yamai, Nijar

Gwamnatin Nijar da kanta a ta bakin Ministan ayyukan jinkai Lawan Magaji, ta tabbatar da cewa dubban gidaje da dimbin dukiyoyi ne suka salwanta a ‘yan makonnin nan a sakamakon ambaliyar ruwan da ta afkawa jihohi 8 na wannan kasa saboda haka ta fara yunkurin tallafawa wadanda abin ya shafa.

Sai dai fa sakataren kungiyar FPN Son Allah Dambaji na cewa ba girin girin ba ta yi mai. “ Duk abin da aka fitar da sunan wadannan bayin Allah, to ya zamanto cewa ya kai ga hannunsu.” A cewarsa, sau da yawa akan fitar da zunzurutun kudi don taimakon jama’a amma idan an bincika sai a gane cewa bai kai garesu ba.

Lura da yadda galibin tallafin kungiyoyi ke tsayawa a manyan birane idan irin wannan lokaci na bukatar agaji ya zo, ya sa masu kare hakkin jama’a kiraye-kiraye don ganin ba a manta da jama’ar karkara ba a wannan karon.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da masana suka bayyana a sahun wadanda za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya a yayin daminar bana, abinda ke nufin bukatar a kwana da shiri don takaita barnar da wannan bala’i ka iya haddasawa.

To amma abubuwan da suka faru da talakawa a ‘yan kwanakin nan na nunin cewa gwamnati ta yi kwance da kaya, in ji Abdou Alhaji Idi.

Yanzu haka jama’ar Nijar na cikin fargaba bayan da ma’aikatar hasashen yanayi ta kasa ta sanar cewa za a fuskanci saukar ruwan sama ba kakkautawa a illahirin yankunan wannan kasa daga ranar 9 zuwa 11 ga watan nan na Agusta saboda haka za ta yiwu a fuskanci ambaliya in dai ba wani gyara na Allah ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG