Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sunan Wani Mamaci Ya Bayyana A Jerin Sunayen Wadanda Suka ci Jarabawa


A Jamhuriyar Nijer, jarabawar ajin karshe a makarantun share fagen shiga jami’a da aka gudanar a tsakiyar watan nan na Yuli ta bar baya da kura bayan da  wata cibiyar jarabawa ta bayyana sunan wani dalibin da ya rasu a jerin wadanda  suka yi nasara.

Koda yake kawo yanzu ba a bayarda wasu alkaluma dake tantance adadin daliban da suka yi nasara a jarabawar BAC ta shekarar 2018 a hukunce ba, bayanai daga kungiyoyin kare hakkin jama’a a fannin ilimi na cewa wannan jarabawa tayi muni sosai saboda wasu dalilai da ake alakantawa da rashin sanin makamar aiki kamar yadda shugaban kungiyar CODE Amadou Roufai Salao ke kokawa akai.

Ministan ilimi mai zurfi Yahouza Sadissou ya dora alhakin wannan koma bayan akan tarzomar da ta dabaibaye sha’anin karatu a tsawon shekara koda yake shi da kansa ya yi amannar cewa jarabawar ta bana tayi tsauri.

Wani abinda ke kara daurewa jama’a kai shine yadda aka bayyana sunan wani dalibin da ya dade da rasuwa a jerin sunayen daliban da suka ci jarabawa bayan wasu misalai na daban dake haifarda shakku a zukatan jama’a.

Hukumomin ilimi na ganin wannan a matsayin wata tangarda ko kuma kuskure irin na dan’adam da ba za a rasa fuskanta ba jefi-jefi.

Dalibai sama da 60000 ne suka halarci azuzuwan jarabawar BAC a bana kuma a Yanzu haka jami’ai sun dukufa ga tattara bayanai daga cibiyoyin jarabawar yankuna 8 na kasar Nijer saboda haka ake sa ran bayarda kammalallen sakamako nan da ‘yan kwanaki masu zuwa inji ministan ilimi mai zurfi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG