Irin sakwannin da wasu alhazan jamhuriyar Nijer ke aika wa ‘yan uwansu ta hanyar kafafen yanar gizo, na nuna bacin rai akan halin rashin tabbas din da suka shiga akan maganar mayar da su gida bayan kammala aikin hajji.
Wakilin hukumar dake kula tsare tsaren aikin hajji na Nijer Alhaji Bukari Sani Zilli kuma mai wakiltar kamfanin zirga zirgar jiragen sama na jirgin saman Max Air ya ce jirgin zai fara kwashe alahazan Nijer daga ranar 6 ga watan nan na Satumba.
'Yan rajin kare hakkin jama’a da suka hada da shugaban kungiyar MAP Lawali Adamou sun gargadi hukumomi akan bukatar daukar wasu mahimman matakai kan mayar da alhazan Nijer.
Wasu jaridun Nijer sun ruwaito cewa wasu alhazan a kalla su 3000, sun shafe kawanaki da dama basu ci abinci ba.
Facebook Forum