Yayin da gwamnatin APC ke cika shekaru biyu da hawa kan karagar mulki a Najeriya, babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Neja ta ce babu wani ci gaba da aka samu ta fuskar gudanar da ayyukan raya ‘kasa a jihar.
Sanannan 'dan wasan kwaikwayon siniman nan, 'dan kasar Birtaniya Roger Moore, wanda akafi sani cikin fina-finan da yayi a matsayin James Bond, ya mutu yana da shekaru 89.
Birtaniya ta kure mizanin barazanar kai mata harin ta’addanci, inda ta tura dakarun soja domin su taimakawa ‘yan sanda, a cewar Fara Minista Theresa May jiya Talata.
An zabi tsohon ministan lafiya na ‘kasar Ethiopia Tedros Adhanom Gheybreysus, a matsayin shugaban hukumar lafiya ta Duniya, WHO. Tedros ya lashe zaben ne a zagaye na biyu lokacin da aka kada kuri’ar jiya Talata. Inda ya kada abokan takararsa David Nabarro na ‘kasar Birtaniya da Dakta Sania Nishtar likatan zuciya na ‘kasar Pakistan.
An gabatar da kuduri gaban Majalisar Dattawan Najeriya, da ke bukatar ‘daukar matakan kare kai daga farmaki ta yanar gizo da kuma yada jita-jita ta kafafen sadarwa na zamani.
Gwamnatin Najeriya ta nuna alamun kyautatuwar alkaluman tattalin arziki a daidai lokacin da talakawa ke kokawa kan tsadar rayuwa. Sai dai kuma wasu daga cikin ‘yan kasauwar sunce su basu fara gani a kasa ba.
Wani rahoto da aka buga a mujallar aikin jinyar kananan yara ya shawarci cewa, bai kamata a ba kananan yara kasa da shekara daya ruwan lemun kwalba ba, sai da izinin likita, kamata ya yi a ba kananan yara ruwan nono ko kuma madarar jarirai.
Kamar arewa maso gabashin Najeriya, wadansu sassan Nijar na fama da karancin abinci sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram. Duk da yake ba a ayyana yunwa ba, karancin abinci da kuma rashin abinci mai gina jiki wata matsala ce da ake fuskanta zahiri.
‘Yan sandan Birtaniya sunce a kalla mutane goma sha tara aka kashe wadansu hamsin kuma suka ji raunuka a wata fashewa da ta auku jiya Litinin a kofar wani dakin wasa a Manchester, Ingila.
Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da aikin bincike akan mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi, bisa zarge zarge guda 8 wadanda suka hada da tuhumar kashe kudaden masarautar ba bisa ka’ida ba.
Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ziyarci jihar Borno don mika tallafin iri na shuka masu inganci ga manoman da rikicin Boko Haram ya shafa a jihar.
Yanzu haka an sake tura ‘karin jami’an tsaro zuwa yankin Takum da Ussa na jihar Taraba, biyo bayan kazancewar rikicin Fulani makiyaya da kuma yan kabilar Kuteb manoma.
Shugaban Turkiya Racep Tayyib Erdogan ya fadada dokar ta baci a hukumance da aka kafa bayan wani juyin mulki a shekarar 2016 da bai yi nasara ba, yana cewar za a ci gaba da wannan dokar har sai kasar ta samu cikakken kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya a nahiyar Afrika, ta rawaito cewar a kwai alamomi masu kwantar da hankali wurin yaki da yaduwar cutar Ebola a Demokaradiyar Jamhuriyar Congo.
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya yana shirin gudanar da wani taron gaggawa a gobe Talata, a matsayin daukar mataki ga gwajin makami mai lizzami da Koriya ta Arewa ke yi.
Tsohon babban hafsan hafsohin sojojin ruwan Najeriya, vice admiral Usman Jibrin, ya aikawa mukaddashin shugaban Najeriya takardar korafi kan hukumar EFCC.
An kammala taron fadakar da manoma game da aikin yashe madatsu da magudanan ruwa a jihohin Kano da Jigawa da kuma wasu sassa na jihar Bauchi, wadanda ke karkarkashin kulawar hukumar kula da koramun Hadejia da Jama’are mai hedikwata a Kano.
Rahotanni da ke fitowa da ga karamar hukumar Askira/Uba dake jihar Borno, na nuni da cewa wasu mahara da ke kyautata tsammanin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a daren Asabar kan wani ‘kauye da Mussa, inda su kayi ta musayar wuta da mutanen ‘kauyen.
Gwamnatin jihar Adamawan dake cikin jihohi uku da rikicin Boko Haram yafi shafa, ta musanta zargin cewa ta soma korar yan gudun hijiran dake jihar.
Domin Kari