Bankin Duniya bisa hadin gwiwa da gwamnatin tarayyar Najeriya ta hannun ma’aikatar ruwa ta tarayya ne zasu gudanar da aikin a wani mataki na magance matsalolin da ke dakile bunkasar ayyukan Noma, musamman ma lokutan rani.
Babban jami’i a ma’aikatar ruwa ta tarayya Injiniya Mohammad Sani Bala, ya ce makasudin wannan taro dai shine kokarin fadakar da manoma da hukumomi kan aikin da gwamnatin tarayya ke yi na Triming a jihohin Kano da Jigawa, inda ake kokari sanar da manoma cewa ana dab da fara gyara-gyaran fadamu da koguna da kuma kayayyakin noman rani a jihohin.
‘karkashin shirin yashe madatsu da magudanan ruwan na karkashin tafkin Hadejia da Jama’are, an tsara bada tallafi ga manoma da aikin zai shafi gonakinsu. Injiniya Nasiru El-Mansur, na hukumar kula da koramin Hadejia da Jama’are, ya ce ya zama dole idan aka zo gudanar da aikin za a rufe ruwa a shiya-shiya, wanda hakan zai dakatar da aikin noma ga wasu manoma, kuma za a basu wani tallafi da zai taimaka musu.
Malama Aisha Isma’il, dake zaman babban jami’ar karbar korafe-korafen manoma ta shirin aikin yashe madatsun da ake yiwa lakabi da Triming ta ce sun sami sukunin warware korafe-korafe kimanin dubu goma tun farkon bude ofishin na ta a watan Janairun wannan shekara.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum