Da yake bayanin gabatar da kudurin gaban Majalisa, shugaban kwamitin fasahar na’ura mai kwakwalwa na Majalisar Dattawa, Buhari Abdulfatai, ya ce yawancin kalubale musamman ma a nahiyar Afirka, yawancin ma’aikatu basa kuda da na’urorinsu masu kwakwalwa da tsaresu daga masu kutse.
Wannan dai ba shine karo na farko da ake gabatar da irin wannan kuduri gaban Majalisar ba, sai dai wannan kudurin ya mayar da hankali ne wajen kariya da satar muhimman bayanai da suka shafi tsaro da kudi da sauran asiran ‘kasa.
“ya dace mu dau matakan rigafi ya fi magani, don ko manyan kasashe irinsu Amurka da Rasha na sa kafar wando ‘daya a wannan yaki.” Inji Sanata Abdulfatai.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Ahmed Lawal, ya ce shima an yada bayanai a yanar gizo dake nuna wai matasa sun yi kememe sun hana shi shiga mazabarsa ko garinsu Gashua a jihar Yobe.
Irin wannan kuduri dai ya taba shan ‘kasa lokacin da Sanata Bala Ibn Na'Allah, ya kai shi zauren Majalisa da neman ‘daukar mataki kan masu cin zarafin ‘yan siyasa da yada kalaman batanci.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Facebook Forum