Cikin takardar korafin da ya mikawa Farfesa Yemi Osinbajo da kuma shugabannin rundunonin sojan ‘kasar, ya yi korafin cewa wasu masu fada a ji na amfani da hukumar EFCC domin gallaza masa.
Ya ce lokacin da yake shugabancin rundunar sojojin ruwan Najeriya, sun kama manya-manyan jiragen ruwa guda 60 makare da gurbataccen mai na sata da suka mika su ga hukumar EFCC, inda ya kalubalance ta da su fito su yi bayanin inda suke ko kuma yanda aka yi da su.
Admaral Usman Jibrin, ya yi mamakin duk wadancan mutane da suka kama da laifin satar Mai an sake su, in banda mutane biyu da aka gabatar gaban kotu a watan Fabarairun wannan shekara. Ya ce wadancan mutane masu fada aji da ya hana yin rawar gaban hantsi da dukiyar Najeriya sune suka tsagayo ta bayan gida suna kokarin yakarsa.
Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin ita hukumar EFCC kan wannan korafi, amma kakakin hukumar Mista Wilson Uwujaren, ya ce shi bai ga wata takardar korafin da zai mayar da martani a kai ba.
Inda ya ci gaba da cewa yanzu abin da ya sani shine akwai magana tsakaninmu da wancan mutumin a gaban kotu. Ya kuma ‘kara da cewa babu wasu mutane da ke juya hukumar EFCC.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum