Babban kamfanin sayar da kayayyaki ta yanar gizo a ‘kasar China, JD.com, ya sanar da shirinsa na kirkirar kananan jiragen nan masu tuka kansu, Drone, da zasu iya daukar kayan da suka kai nauyin tan ko sama da haka domin ya rinka kai sakonni ga mutane.
Kamfanin ya ce zai gwada jiragen drone ta wata hanyar sadarwa da yake kirkira wadda zata yi aiki a fadin Arewacin gundumar Chaanxi. Haka kuma jiragen zasu yi dakon kayan zuwa kauyuka, su kuma dauko kayan amfanin gona zuwa birane.
Hedikwatar kamfanin JD.com dake birnin Beijing, ta sanar da cewa kananan jiragen zasu fara ‘daukar kaya suna isar da su ga mutane cikin watan Nuwamba mai zuwa. Sauran kamfanonin masu sayar da mahaja ta yanar gizo irinsu Amazon.com yanzu haka suna gwajin fasahar jiragen drone.
Shi dai kamfanin JD.com na harkokin kasuwancinsa ne a duk fadin kasar China, wanda ke da ma’aikata dubu 65. Kamfanin ya ce yanzu haka yana da kwastomomi miliyan 235.
Samar da kananan jiragen drone wata hanya ce ta shawo kan matsalolin isar da kayayyaki ga kwastomomi dake yankunan karkara.
Yin amfani da jiragen drones don dakon kayayyaki a China da wasu kasashe na fuskantar kalubale, ciki harda na ka’idojin tafiya a sama da kuma hanyoyin da za a kaucewa arangama da tsuntsaye. A Amurka ana iya barin kananan jirage na ‘yan kasuwa su yi amfani da sararin samaniya ne kawai don gwaji.