Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Sake Taron Gaggawa Kan Gwajin Makamin Da Koriya Ta Arewa Ta Yi


Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un.

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya yana shirin gudanar da wani taron gaggawa a gobe Talata, a matsayin daukar mataki ga gwajin makami mai lizzami da Koriya ta Arewa ke yi.

Ofishin jakadancin Uruguay a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce Amurka da Koriya ta Kudu da Japan ne suka kira wannan zaman.


Koriya ta Kudu tace an harba makami mai lizzami daga gundumar Kudancin Pyeongan wanda ya tashi ya yi tafiyar kilomita 500 kafin ya fada tekun Japan.

Wannan shine gwaji na biyu da Koriya ta Arewa tayi a cikin wannan mako kuma shine ya kai gwaje gwajen makaman Korea ta Arewa goma a cikin wannan shekara


Wata sanarwar hadin gwiwan manyan hafsoshi na sojojinmu na lura da alamomin karin takala da sojojin Korea ta Arewa ke yi, su kuma sojojinsu na kan shirin ko takwana


A wani martani ga gwajen gwajen farko da Korea ta Arewa ta yi, shugaban Amurka Donald Trump ya tura rundunar mayakan ruwa zuwa ruwayen yankin Koriya a matsayin kashedi gwamnatin kwaminisanci don ta kawo karshen shirinta na makaman nukiliya.


Amma dai sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya musunta cewar matsin lamba Amurka ke yiwa Korea ta Arewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG