Alkaluman da hukumar bada agajin gaggawa ta bada a yau Laraba, hukumar ta ce adadin wadanda suka mutu a wannan tagwayen harin kunar bakin wanken sun karu zuwa mutum 30, baya ga wadanda aka garzaya da su zuwa cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya, wato FMC Yola.
Imam Abbani Garki, dake zama jami’in hukumar ta NEMA, mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana halin da ake ciki tare da karyata rahotannin da wasu kafofin yada labarai suka bada dake cewa fiye da mutum 60 ne suka mutu.
Ya zuwa yanzu dai tuni gwamnan jihar Adamawan Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya kira wani taron gaggawa kan harkar tsaro domin gano bakin zaren magance irin wannan tashin hankali.
Ahmad Sajo shine kwamishinan yada labaran jihar Adamawa, ya ce kawo yanzu ba wata kungiya data dau alhakin wannan hari na garin Mubi, yayin da mazauna garin ke danganata shi da irin hare haren da yan kungiyar Boko Haram suka sha kaiwa a baya.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum