A lokacin da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya kaiwa shugaban Amurka Donald Trump ziyara a farkon makon nan, tawagarsa ta gana da kusoshin kamfanin Boeing mai ke jiragen sama, domin tabbatar da shirin bude sabon kamfani a Najeriya.
Da yake zantawa da Muryar Amurka Ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Alhaji Hadi Sirika, ya ce basa fatan idan an kafa sabon kamfanin ya yi sanadiyar durkusar da sauran kamfanonin jiragen sama da ake da su yanzu haka a kasar, maimakon haka ya kawo sabon tsari ga harkar sufurin don samar da ci gaba.
Babban batun da yafi ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya shine rashin tabbas ga yadda jiragen saman kasar suke, domin wasu lokuta jirage kan bata lokuta masu tsawo kafin su tashi, har ma takan kai ga wasu lokuta an soke tashin jiragen ma baki daya.
Minista Hadi Sirika, ya ce da yardar Allah irin wannan bata lokaci zai zamanto labari nan bada dadewa ba.
Domin karin bayani saurari tattaunawar Aliyu Mustaphan Sokoto da Ministan Sufurin Jiragen saman Najeriya, Alhaji Hadi Sirika.
Facebook Forum