Makasudin ganawar shugabannin biyu ita ce tattauna hanyoyin da kasashensu za su karfafa dangantakar da ke tsakaninsu, da ta hada da habaka tattalin arziki da yaki da ta’addanci da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro.
A ranar Litinin 30 ga watan Afrilu, shugabannin za su zauna daga bisani kuma su ci abincin rana tare inda za su ci gaba da tattaunawa
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da fadin albarkacin bakinsu game da wannan ziyara da shugaba Buhari zai kai Amurka, inda wasu ke ganin wannan ziyara wata hanya ce da Amurka za ta iya taimakawa Najeriya a fannin tattalin arziki da samar da tsaro.
A baya dai Amurka ta yi kokwanton sayarwa da Najeriya makamai, bisa zargin dakarun kasar na danne hakkin bil Adama a daidai lokacin da mayakan Boko Haram ke cin karensu ba babbaka.
Amma, bayan da shugaba Trump ya hau mulki, gwamnatinsa ta amince da sayarwa da Najeriya jiragen yaki na zamani da ake kira A-29 Super Tucano har guda 12.
Saurari tataunawar da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya yi da wasu ‘yan Najeriya.
Facebook Forum