Matasa a jihar Bauchi sun kona sakatariyar karamar hukumar Ningi jiya Asabar, saboda sun shafe sa’o’i suna jiran a gudanar da zaben shugabanni a matakin unguwanni a jam’iyyar APC, amma ba a yi ba.
A cewar wani mutum dake gurin da abin ya faru ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa, dadewar da mutane suka yi suna jira a gudanar da zabe har zuwa bayan karfe uku, lokacin da ake shirin yiwa mutanen jawabi, sai wasu suka harzuka suka cinnawa ginin sakatariyar wuta.
Daraktan sashen gudanar da mulki na karamar hukumar Ningi, Kabiru Abdullahi Mohammad, ya tabbatar da batun kona wasu sasssan ginin kamar hukumar. Inda ya ce sun dauki lokaci kafin su shawo kan wutar.
Mai ritaya Ahmed Tijjani Baba Gamawa ya ce an bayar da duk takardun zaben ake bukata don cikewa bayan da aka tayar da jijiyar wuya, amma kuma ba a yi zabe ba saboda rashin bada takardun kan lokaci kamar yadda dokar zaben jam’iyya ta tanada.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Abdulwahab Muhammad.
Facebook Forum