A baya-bayan nan dai wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja ta sake bayar da umarnin a saki Sambo Dasuki, amma har ya zuwa yanzu gwamnati ta yi buris da umarnin kotun.
Da yake magana da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya ce bincike ne ya fadada, inda aka gano cewa an samu asarar rayuka masu yawa duk a dalilan tauyewa ma’aikatan tsaro hakkinsu na rashin basu kayan aikin da suka kamata don gudanar da aikin da ya kamata.
Gwamnatin ta yi watsi da umarnin kotu ne kasancewar ta yi amfani da mizanin hakkin al’ummar Najeriya da aka tauye.
Domin karin bayani saurari hirar Aliyu Mustaphan Sokoto da Abubakar Malami.
Facebook Forum