Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas: Taron Inganta Adabin Baka a Nahiyar Afirka


'Yan Wasan Kokawar Gargajiya A Kasar Jamhuriyar Nijar
'Yan Wasan Kokawar Gargajiya A Kasar Jamhuriyar Nijar

An kamala wani taron kasa da kasa domin inganta adabin baka na yankin nahiyar afrika, taron da kungiyar raya adabin baka ta duniya ta dauki nauyin gudanar dashi a birnin Lagos.

Manufar taron shine inganta adabin baka na al’adun afrika da yanzu haka ke fuskantar bacewa ko gurbacewa saboda da rungumar al’adun kasashen waje irin na turawa da matasa ke yi.

Anfani da na’urorin sadarwar zamani ko kuma sakaci daga magabata da hukumomi dake yiwa al’adun Afirka rukon sakainar kashi.

Daya daga cikin wadanda suka gabatar da kasidu a taron, Farfesa Sarah, dake zama kwararriya akan adabin baka na nahiyar Afrika ‘yar kasar Faransa, wadda kuma ta gudanar da bincike a jami’ar Paris inda ta yi aiki a kasashen Guinea da Mali da Burkina Faso akan wakokin adabin al’ummar kasashen, ta gano muhimancin su kamar yadda bincikenta ya nuna.

Farfesa abubakar aliyu liman shehun malami ne a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ya ce ganin yadda al’adun Afirka ke neman bacewa a wannan zamanin, hakan yasa suka yanke shawarar tashi tsaye domin magance matsalar.

Yanzu dai a kokarin da gwamnati keyi na dawo da rajar al’adu da sanin tarihin kasa a tsakanin matasa, gwamnatin Najeriya ta dawo da koyar da tarihi a makarantu.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG