Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Bakin Haure 100 Sun Mutu a Tekun Bahar Rum


Bakin haure daga nahiyar Afirka kan hanyarsu ta zuwa Turai.
Bakin haure daga nahiyar Afirka kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Bakin haure sama da 100 sun mutu bayan da kwalekwalen balam-balam da ke dauke da su guda biyu su ka samu matsala a cikin tekun Bahar Rum bayan sun baro gabar Libiya a farkon wannan wata na Satumba.

Kungiyar likitoci masu shiga kowace kasa aikin agaji, Doctors Without Boarders da Turance, ta fada a wani rahoton da ta saka a dandalinta na intanet ranar Litini cewa akasarin bakin hauren sun fito ne daga kasashen Sudan da Mali da Najeriya da Kamaru da Ghana da Libiya da Aljeriya da Masar.

Wadanda su ka rayu kuma kungiyar agajin ke masu jinya sun ce daya daga cikin jiragen ya samu matsalar inji, a yayin da dayan kuma ya sace har ya fara nitsewa.

"Yara sama da 20 ne su ka mutu, ciki har da wasu tagwaye 'yan watanni 17," abin da rahoton ya ruwaito wadanda su ka rayu ke cewa kenan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG