Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Za Ta Ba Da Hadin Kai Ga Kotun Kasa Da Kasa Ba Kan Yakin Afganistan


Dakarun Amurka
Dakarun Amurka

Amurka, jiya Litini, ta ce ba za ta ba da hadin kai ba ta kowace fuska ga Kotun Kasa da Kasa ta Shari'ar Manyan Laifuka dake birnin Hague, muddun ta gudanar da bincike kan zargin aikata laifukan yaki da ake ma sojojin Amurka da kuma jami'an leken asirinta a kasar Afrghanistan.

Mai Bayar da Shawara ga Kasa Kan Harkokin Tsaro John Bolton ya gaya ma wata kungiyar rikau mai ra'ayin fedaraliyya a birnin Washinton DC cewa kotun ba ta ma da hurumi kan Amurka da mutanen kasashen da ba su rattaba hannu kan yarjajjeniyar kafa kotun a 2002 ba.

A lokaci guda, Bolton ya ba da sanarwar cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka za ta rufe wani ofishin Kungiyar gwagwarmayar 'yantar da Falasdinu (PLO) a birnin Washington DC a matsayin martanin kudurin Falasdinawa na ganin kotun ta hukunta Isira'ila, saboda kuma Falasdinawa sun ki tattaunawa kai tsaye da kasar Isira'ila kan batun zaman lafiya.

Babban jami'in Falasdinu Saeb Erekat ya ce barazanar rufe ofishin da gwamnatin Trump ta yi ba za ta tsorata gwamnatin Falasdinu kan aniyarta ta maka Isira'ila a kotun duniya ba. " 'Yancin Falasdinawa ba abin cafanarwa ba ne, don haka ba za mu mika wuya ga barazana da ingizawar da Amurka ke yi ba," a cewar sa jiya Litini.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG