Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rwanda: Paul Kagame Ya Yi Wa Shugaban 'Yan Adawar Kasarsa Afuwa


Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya yiwa shugaban ‘yan adawar kasar dake daure afuwa, Victoire Ingabire Umuhoza.

An bayyana afuwar ne a wata sanarwa da gwamnatin Rwanda ta fitar da yammacin jiya Juma’a, wanda ke zama wani bangare yiwa masu laifi 1,140 afuwa.

Wani mutum da ya samu afuwar shugaban kasa, shine fitaccen mawakin nan mai suna Kizito Mihigo.

Sanarwar dai na cewa, shugaban kasa yayi anfani da ikonsa na shugaban kasa wajen yin afuwar, biyo bayan rubuta takardar neman afuwa da masu laifin suka yi cikin watan Yunin da ya gabata.

Kundin tsarin mulkin kasar Rwanda ya baiwa shugaban kasa ikon amfani da mukaminsa wajen yiwa masu laifi afuwa ta hanyar da doka ta tsara, bayan ya tuntubi kotun kolin kasar.

Wasu lokuta gwamnatin Kagame kan zargi kungiyar ‘yan FDLR da hannu a kisan kare dangin da ya faru a kasar tun shekarar alif 994, inda aka kashe dubun dubatan ‘yan Rwanda cikin kwanaki 100.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG