Guterres ya shaidawa manema labarai jiya Talata cewa, “Idlib ne gari daya tilo da ya rage daga cikin yankunan da aka haramta tada hankali a Syria, kuma bai kamata a maida wurin wurin da ake zubar da jini ba.”
Kimanin farin kaya miliyan uku ne ke zaune a arewa maso yammacin yankin, kuma MDD ta sha gargadin cewa za a jefa al’umma cikin matsanancin kuncin rayuwa idan aka kai harin soji a wurin.
Rasha da Iran da kuma Turkiya sune aka dauka a matsayin kasashen dake tabbatar da kiyaye yarjejeniyar haramta bude wuta a yankin. Sune suka sa ido wajen kulla yarjejeniyar kebe yankunan a Syria da zai zama mafi kwanciyar hankali ga farin kaya. Yankunan sun hada da Idlib, da Hama da gabashin Gouta da kuma kudancin Syria. A halin yanzu dai, Idlib kadai ta rage inda ake kiyaye wannan yarjejeniyar, sojojin sun kwace sauran garuruwan, suka maidasu karkashin ikon gwamnati.
Facebook Forum