Yawan kananan yaran da suka kamu da wata cuta mai shanye jiki yayi yawan da ba a taba gani ba a Amurka. A cewar hukumar hana yaduwar cututtuka ta CDC.
Kotu a Canada na duba yiwuwar ko zata baiwa shugabar katafaren kamfanin fasahar nan na Huawei beli, ya yin da take jiran ganin ko za a mika ta Amurka domin a tuhumeta a can.
Ciki da Gaskiya Wuka Ba Ta Hudashi
Za a ajiye gawar tsohon shugaban kasar Amurka George H.W. Bush a zauren majalisar dokoki Amurka daga yau Litinin da yamma domin ba Amurkawa damar karrama shugaban kasar Amurkan na arba’in da daya.
Babban bankin duniya ya sanar yau Litinin cewa, zai ninka kudin da yake badawa domin tallafawa kasashen dake fama da talauci su iya tunkarar matsalar dumamar yanayin zuwa dala miliyan dubu dari biyu cikin shekaru biyar.
Hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta tura zaratanta kimanin dubu biyu zuwa shiyyar Arewa maso Gabas don yaki kafada da kafada da sojoji karkashin rundunar Operation Lafiya Dole a yakin da ake da mayakan Boko Haram.
Wasu matasa daga jihohin Pilato da Kogi sun bayyana kudirinsu na bijirewa shiga bangar siyasa da haddasa fitina a kasa.
Allah ya yiwa George H.W. Bush tsohon shugaban kasar Amurka rasuwa yana da shekaru 94 a duniya.
Tsaka Mai Wuya
Rasha ta yi harbi kan wadansu jiragen yakin Ukraine guda biyu ta kuma rafkawa na uku a tekun Bahar Asuwad jiya lahadi, suna zargin ‘yan kasar Ukrain da shiga yankin ruwan Rasha ba bisa ka’ida ba.
Hukumomin Amurka sun dakatar da harkokin sufuri kan iyakar Ysidro dake tsakanin San Diego da Tijuana, Mexico bayan da ‘yan ci rani suka yi kokarin bankawa ta kan iyakar jiya Lahadi.
Likitocin kasar Kamaru sun ce aiki yana fin karfinsu, yayin da abokan aikinsu ke tafiya wadansu wurare neman ingancin rayuwa.
Wasu al’ummar jihar Borno sun nuna damuwarsu game da irin hare-haren ta’addanci dake kara ta’azzara akan jami’an tsaro da ma jama’ar da ke kewaye da babban birnin Maiduguri.
Dubban jama’a sun halarci bikin nadin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar, ciki har da tsoffin shugabannin Najeriya da gwamnoni da kuma sarakunan gargajiya
Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump na kokarin rage muhimmancin rahoton nan da aka fitar wanda ya kunshi gargadi mai tsanani kan abin da ka iya faruwa sanadiyyar canjin yanayi a Amurka.
Masu zanga-zangar nuna fushinsu da manufofin gwamnati sun yi arangama da 'yan sanda jiya Asabar a Champs-Elysees da ke birnin Paris, a wani zagaye na zanga-zangar da ake yi ta nuna bijirewa ga Shugaban Faransa Emmanuel Magcron.
An gina wani kauye musamman domin mata a yankin Rojave na kasar Syria. Kauyen da ake kira Jinwar, wanda a harshen Kurdawa yake nufin wurin mata, yana da rukunin gidaje da aka gina iri daya guda talatin.
Kamar yadda alkaluman hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ke nunawa kawo yanzu yan gudun hijiran kasar Kamaru da tashe-tashen hankula dake da nasaba da batun yan aware, ya tilastawa guduwa suna barin garuruwansu sun kai dubu talatin.
Domin Kari