Kakakin rundunar ‘yan sanda Mista Jimoh Moshood, ya ce baya ga yakin da ‘yan sandan zasu yi akwai kuma karin rawar da zasu taka, kamar tsare garuruwa da yankunan da aka kwato da samar da tsaro ga jami'an kungiyoyin agaji da kayan agajin da ma kare sansanonin ‘yan gudun hijira.
Rundunar ‘yan sandan tuni ta tura karnukan da aka horas guda dari don wannan yaki, baya ga ‘yan sandan sama da aka tura suna sintiri da jirage masu saukar ungulu.
Amma wani masanin tsaro kuma tsohon malami a makarantar horas da Hafsoshin sojin Najeriya Dakta Umar Ardo, ya ce shigar yan sandan cikin yakin wannan ba dai dai bane.
Hakan a cewarsa na nuna tamkar sojoji sun gaza ne, domin shekara da shekaru sojoji ke gudanar da wannan yaki, kuma kundin mulkin kasa ma su sojin ya dorawa alhakin wannan aiki.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum